Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasar Iran Islami ya kuma ce; Bisa la’akari da sunan da jagoran juyin musulunci ya bai wa shekarar bana ta; “Samar da ilimi da kuma damammaki na aiki”, Hukumar makamashin Nukiliyar ta Iran za ta kasance a sahun gaba a wannan fage.”
Har ila yau Islami ya kuma ce; Baya ga wutar lantarkin da ake da ita a yanzu, nan gaba za a samar da wata wutar lantarkin daga makamashin Nukiliya da za ta kai megawati 10,000.”
342/